Kashe-Kashe: A sa dokar ta baci a jihar Zamfara kawai - Sanata Dansadau

Kashe-Kashe: A sa dokar ta baci a jihar Zamfara kawai - Sanata Dansadau

Sai'idu Dansadau dake zaman tsohon Sanata da ya taba wakiltar mazafar jihar Zamfara ta tsakiya ya bayyana cewa dokar ta baci ce kawai za a sanya idan dai har ana so a kwao karshen kashe-kashen da ake yi jihar.

Sanata Dansadau ya yi wannan hasashen ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan sa dake a garin Abuja ranar Alhamis din da ta gabata inda ya kuma kara da cewa dukkan wani abu da hakan ba kwaskwarima ce kawai.

Kashe-Kashe: A sa dokar ta baci a jihar Zamfara kawai - Sanata Dansadau
Kashe-Kashe: A sa dokar ta baci a jihar Zamfara kawai - Sanata Dansadau

KU KARANTA: Gidan rawar da maza ke karuwanci a Najeriya

Legit.ng ta samu haka zalika cewa ya bayyana yawan mutanen da aka kashe a jihar da cewa sun kai dubu 3 a ciken shekaru biyu kacal da suka gabata.

Haka zalika ya bayyana cewa gwamnan jihar Abdulaziz yari ya gaza a wajen bayar da kyakkyawan shugabanci a jihar.

A wani labarin kuma, Babban bankin duniya ya nada wani matashi mai suna Muhammad Abdullahi dake zaman kwamishinan tsare-tsare da kuma kasafin kudin gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mamaba a majalisar ta mu'amala da mutane watau Expert Advisory Council on citizen engagement a turance.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta DailyNigerian, Mista Muhammadu Abdullahi, kwararre ne a harkokin tattalin arziki kuma yanzu zai hadu ne da wasu mutane biyar daga sassa daban-daban na duniya domin yin aikin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel