Rikicin kabilanci yayi sanadiyan mutuwar mutane 73 a Taraba
Akalla mutane 73 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan kimanin kauyuka 50 aka gona bayan sabon rikici da ya balle tsakanin Hausa-Fulani da kabilar Yandang a karamar hukumar Lau dake jihar Taraba.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Sahabi Mahmoud ya fadama manema labarai a ranar Juma’a a Jalingo cewa rikicin wanda ya fara a ranar 5 ga watan Yuli yayi sanadiyan mutuwar sama da mutane 23 daga kungiyarsa.
Ya bayyana cewa yan Hausa-Fulani 3000 da suka rasa matsuguninsu, wadda mafi akasarinsu mata ne da kananan yara suna gudun hijira a sakatariyar kungiyar Musulmai a Jalingo da sauran kananan hukumomin dake makwabtaka da su.
Mahmoud ya ce abun takaici tunda marasa galihun suka isa sakatariyar kungiyar Musulunci a Jalingo, babu wani jami’in gwamnati da ya kai masu ziyara ko kuma basu kayayyakin agaji.
A nashi bangaren, wani dattijo na garin Yandang, Mista Aaron Artimas, yace sama da mutane 50 daa yankin Yandandang da sauran kabilu ne suka mutu sakamakon rikicin.
KU KARANTA KUMA: Ka binciki yan sanda kan harin Fayose – Sanatocin PDP ga Buhari
Artimas ya bayyana cewa kabilun Hausa-Fulani, Yandang, Mumuye da Yoti da kuma sauran kabilu sun shafe lokaci mai tsawo suna zaman lafiya a matsayin yan uwan juna ba tare da matsala ba.
Ya daura alhakin rikicin akan wasu mutane daga waje da ke son kawo sabani a siyasance.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng