Na kashe Khadija Oluboyo ne don yin arziki cikin kwana 7 - Saurayinta

Na kashe Khadija Oluboyo ne don yin arziki cikin kwana 7 - Saurayinta

Yayinda bincike ke cigaba da gudana kan al’amarin kisan diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Alhaji Lasisi Oluboyo, da ake zargin saurayinta da yi.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa saurayin da ke hannun jami’an yan sanda yanzu ya aske gashin Khadija ne kuma ya cire farjinta wanda ya kaiwa bokan da ke masa aiki a cikin garin Ondo sannan ya birneta cikin dakinsa.

A daren da ya kasheta, wasu abokansa guda biyu wadanda suka taimaka masa wajen aiwatar da wannan aika-aika.

KU KARANTA:Yadda wani Saurayi ya kashe Budurwar da ake sa rai zai aura saboda neman Duniya

Bayan birneta cikin dakinsa, bokan ya umurcesa ya kwana a cikin dakin na tsawon kwanaki 7 kafin arzikinsa ya zo.

Na tsawon kwanaki shidan da ya birne yarinyar a dakinsa, ya kasance yana amfani da maganin sauro da turare domin kawar da warin da ke fitowa.

Dalilin da yasa makwabta basu farga da abinda yakeyi ba shine sun shagala da kallon kwallo kuma ya kure karan akwatin rediyonsa da waka.

Amma bayan kwanaki shida asirinsa ya tonu. Da ya samu nasarar kwana da gawar na tsawon kwanaki 7, da yayi arzikin da baya tsammani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng