Shegiyar uwa: Mutan unguwa sun waye gari da ganin sabuwar jaririya cikin bola

Shegiyar uwa: Mutan unguwa sun waye gari da ganin sabuwar jaririya cikin bola

Hankalin jama’a ya tashi da safiyar yau Alhamis yayinda wata ta wata mata ta jefar da sabuwar jaririyarta a cikin bola a jihar Legas.

NAN ta bada rahoton cewa an tsinci gawar wannan jaririya ne a bolan tashar Costain dake titin Apapa, Ebute meta, jihar Legas.

Jaririyar na sanye da koren riga da bakin hula kuma ta mutu. Zuwa yanzu ba’a gano mara imanin da ta aiwatar da wannan abin takaicin ba.

Shegiyar uwa: Mutan unguwa sun waye gari da ganin sabuwar jaririya cikin bola
Shegiyar uwa: Mutan unguwa sun waye gari da ganin sabuwar jaririya cikin bola

Wani mazaunin Apapa ya bayyanawa manema labaran da ke wajen cewa ya ga gawar jaririyar tanada sauran rai da safe lokacin da ya nufi wajen aiki. Ba tare da bata lokaci ba sai ya kira hukumar bada agaji na gaggawa na jihar Legas.

Amma duk da kiransu da yayi, ma’aikatan hukumar basu zabura suka karaso wajen a lokaci ba har Allah ya dauki ran jaririyar.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya sabuwar doka kan masu fitsari da ba haya a hanya

Yace: “Ku duba irin wannan abin takaici, da an ceci rayuwar jaririyar an da wuri, da bata mutu ba. Hukumar bada agaji na gaggawa na jihar Legas sun bamu kunya.”

Kakakin hukumar yan sandan jihar, CSP Chike Oti, ya tabbatar da wannan abu kuma yace an sanar da ofishin hukumar yan sandan Iponri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng