Himma bata ga raggo: Kalli hotunan wata budurwa marar hannu amma tana wanki

Himma bata ga raggo: Kalli hotunan wata budurwa marar hannu amma tana wanki

Tabbas Hausawa sunyi gaskiya da suka ce himma ba ta ga raggo sannan kuma nakasa a zuciya take ba'a gangar jiki ba.

Haka ne dai kamar dai yadda muka tabbatar da hakan a kan wata kyakkyawar budurwa mai suna Olivia Malacky da ke yin wanki da kanta duk da nakasar da take tare da ita.

Himma bata ga raggo: Kalli hotunan wata budurwa marar hannu amma tana wanki

Himma bata ga raggo: Kalli hotunan wata budurwa marar hannu amma tana wanki

KU KARANTA: Anfanin namijin goro 7 a jikin dan adam

Legit.ng dai ta samu cewa ita dai budurwar duk da kasancewa ta rasa hannun ta daya a yayin wani mummunan hadari da ya same ta a shekarun baya, ta bayyana cewa ko kadan hakan bata bari ya rage ta da komai ba don kuwa tana yin harkokin ta kamar yadda ta saba dai-dai gwargwado.

Yanzu haka dai budurwar ta dauki nakasar dake tare da ita a matsayin kaddara inda ma ta maida ta tamkar wani kaima gareta kuma ta dage kan zaburar da sauran al'umma masu irin larurar ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel