An hana Musulmai yin Sallar Juma'a a Tajmahal
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa an haramtawa Musulmai yin Sallar Juma'a a Tajmahal da ke garin Agra na kasar Indiya wanda ya kasance daya daga cikin wuraren ban mamaki na duniya.
Jaridar Indian Times ta rawaito cewa, Kotun Kolin Indiya ce ta aiwatar da wannan hukunci na cewa, Tajmahal na daya daga cikin wurare 7 na duniya masu ban mamaki a saboda haka dole ne a bashi kariya.
Kotun ta ce, akwai masallatan Juma'a da dama a Agra. Masu son yin Sallah sai su rankaya can su gudanar da ibadar su.
Hukuncin ya kuma bayyana cewa, dukkan masu son yin Sallah a Masallacin da ke Tajmahal dole su nuna shaidar cewa, suna rayuwa a garin Agra.
KU KARANTA KUMA: Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja
A shekarar 1631 ne Shah Jihan ya gina Tajmahal karkashin Daular Hint-Turk.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng