Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja

Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar layin dogo da tashan jirgin kasan birnin tarayya Abuja a yau Talata, 12 ga watan Yuli.

A wani jawabi da shugaban kasar ya wallafa a shafin sada zuminta na Facebook ya bayyana cewa wannan hanyar sufuri ne wanda zai saukaka rayuwa ga mazauna birnin tarayya tare da habbaka tattalin arziki.

Ga cikakken jawabin nasa: “A safiyar yau na kaddamar da tashan jirgin kasa na Abuja. Kammala wannan muhimmin aiki ya kasance mafarki da ya zama gaskiya, annan kuma ya nuna karara cewa gwamnatinmu ta jajirce wajen yin ingantattun ayyuka.

Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja
Cikakken jawabin shugaba Buhari a wajen kaddamar da tashan jirgin kasan Abuja

Tashan jirgin Abuja tabbaci ne na cewar mu gwamnati ne masu cika alkawaranmu. Tashan jirgin kasa na zamani zai habbaka tattalin arzikin birnin tarayya da kawo inganci ga rayuwar jama’a.

KU KARANTA KUMA: An binne mutane 32 da yan fashi suka kashe a Sokoto (hoto)

Jajircewarmu wajen ganin an mallaki tsarin jirgin kasa na zamani a Najeriya ya kammala. Rukunin tashar jirgin saman Abuja na biyu zai sada birane da dama, yayinda lamarin safara a jirgin kasa ke gyaruwa, a yanzu haka na Lagas-Ibadan na nan ana aiki a kai.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng