Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi

Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi

Rundunar yan sandan jihar Kebbi a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa wani makiyaya ya kashe wani dan sanda, Umaru Danladi a Kaoge dake karamar hukumar Bagudo na jihar.

An tattaro cewaan kama makiyayin, Babuga Kuaara, kan laifin, sannan kuma cewa dan sandan ya kasance wanda ke aiki a hukumar yan sandan Kaoje dake karamar hukumar ta Bagudo.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa wani manomi a yankin wanda yayi ikirarin cewa makiyayin ya kai dabbobinsa gonar shi domin suyi masa barna a yammacin ranar Laraba ne ya kai kara ofishin yan sandan.

Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi
Makiyayi ya kashe wani sufeton dan sanda a Kebbi

Wani idon shaida da ya nemi a boye sunansa ya fadama manema labarai a ranar Alhamis cewa “Wani jami’in dan sanda na Kaoje ne aka umurta da ya je ya kama makiyayin dake shawagi da dabbobinsa a yankin.

“Jami’in dan sandan wadda ya zo da bindigarsa ya kama mai laifin, amma a lokacin da yake jan shi zuwa wajen da ya ajiye motarsa, sai makiyayin ya soki jami’in da wuka a wuyarsa.

“Mun ga jami’in yana ta birgima cikin guranani da jinni, amma ya mutu kafin mu bashi agajin gaggawa.”

KU KARANTA KUMA: Marigayi Audu Abubakar ne ya bamu bindigogi – Yan fashi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa anyi jana’izzar mutane da yawa a kauyen Tabbannin Gera dake Sokoto bayan yan fashi sun kashe mutane 32 a kauyuka hudu na jihohin Sokoto da Zamfara.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ba iyalan wadanda abun ya cika da su tabbacin daukar mataki a Rabah domin magance matsalar da kuma tabbatar da sun koma kauyukansu.

Gwamnatin jihar ta kuma rarraba kayan agaji na miliyoyin naira ga wadanda abun ya shafa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel