Yadda wasu ‘yan mata 2 suka sace ATM din kawarsu suka cire kudi har N365,000, amma mai ya faru?

Yadda wasu ‘yan mata 2 suka sace ATM din kawarsu suka cire kudi har N365,000, amma mai ya faru?

- 'Yan mata biyu sun hada baki wajen sace katin cirar kudin kawarsu

- Bayan sun kashe kudin ne gabadaya sai asirinsu ya tonu

- Amma kuma sun gaza biyan kawar tasu kudinta hakan ta sa har aka ji kansu

A ranar Alhamis din nan ne aka gurfanar da wasu 'yan mata masu suna Hope Eze mai kimanin shekaru 23 da kuma Ugonma Chikezie yar kimanin shekaru 30, a gaban kotun majistire dake jihar Legas bisa zarginsu da satar katin cirar kudi na ATM na wata kawarsu tare da cire kudi kimanin Naira 365,000 daga asusun ajiyarta.

Kaka-kara-kaka: ‘Yan mata 2 sun sace ATM na abokinsu sun cire kudi har N365,000, amma abinda ya faru da su daga baya yayi daidai
Kaka-kara-kaka: ‘Yan mata 2 sun sace ATM na abokinsu sun cire kudi har N365,000, amma abinda ya faru da su daga baya yayi daidai

Eze dai ta kasance mai sana'ar gyaran gashi ce yayinda ita kuma Chikezie tana harkokin kasuwanci, dukkaninsu mazauna rukunin gidaje ne na Gowon da ke unguwar Egbeda.

Dan Sanda mai gabatar da kara sufeto Victor Eruada ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 10 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Budurwa mai Digiri 2 mai shekaru 40 ta kashe kanta a saboda an dame ta tayi aure

Ya kara da cewa mai kudin Ruth ta gano kawayenta ne suka aikata mata satar, sai ta bukaci da su dawo mata da kudin da suka sace mata, inda su kuma suka shaida mata tuni sun kashe kudin amma za su biya ta zuwa wani lokaci.

Duk wani kokari na ganin sun biya kudin ya ci tura, wanda kuma hakan ya saba da sashe na 287 da kuma na 411 na kundin laifuffuka na jihar Lagos, kuma aikata hakan zai iya sabbaba yankewa wanda ya aikata hukuncin zaman shekaru uku a gidan yari.

A karshe alkalin kotun Jastis M. I Dan-Oni ya bayar da belin wadannan yan matan akan Naira dubu dari tare kuma da gabatar da mutane biyu ma'aikatan jihar Lagos masu shaidar biyan haraji na shekara 2 da za su tsaya musu.

Ya dakatar da sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel