Lafiya jari: Anfanin namijin goro 7 a jikin dan adam da baku sani ba

Lafiya jari: Anfanin namijin goro 7 a jikin dan adam da baku sani ba

Namijin goro dai wani icce ne da Allah ya yiwa matukar farin jini musamman ma a Nahiyar Afrika da sauran kasashen bakaken fata inda akan samu masu tu'ammali da shi sosai.

Shi dai Namijin goro yana kama ne da kuriga amma yana da matukar girma wanda wanin shi ma yakan kai tsawon murabba'I 3 zuwa 5 a ma'aunin Sentimita.

Legit.ng ta samu cewa duk da cewar yana da daci sosai, amma ko kadan hakan baya hana mutane tu'ammali da shi saboda matukar anfanin sa a jiki.

Lafiya jari: Anfanin namijin goro 7 a jikin dan adam da baku sani ba
Lafiya jari: Anfanin namijin goro 7 a jikin dan adam da baku sani ba

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya raba EFCC 2

Ga dai wasu daga cikin anfanukan nasa nan mun tattaro maku:

1. An ce yana maganin masassarar cizon sauro

2. Haka ance yana maganin cututtukan da suka shafi huhu da iska

3. Bincike ya nuna yana maganin ciwon ido

4. Ga 'yan mata masu kwalisa kuwa, Namijin goro na rage kiba

5. An ce yana kare mutane daga daukar cutar kanjamau

6. Namijin goro kamar yadda bincike ya nuna yana magance matsalar rashin haihuwa

7. Haka ma ance yana maganin ciwon gabobi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng