Asirin wata budurwa da ta saci jaririn sati 3 da haihuwa ya tonu, duba hoton
- Son haihuwa ido rufe ya sanya wata mata satar dan jinjiri
- Sai dai kuma mai gidanta ya dago lagonta har ma ya kai karar ta wurin 'yan sanda
- Yanzu haka dai 'yan sanda sun yi ram da ita
Matar mai suna Bunmi Adebayo mai kimanin shekaru 26, ta bayyana cewa babban dalilin da ya sanyata wannan aikata danyen aikin "Yau shekarata goma da yin aure, amma shiru ban samu haihuwa ba, wanda hakan ya sanya ni cikin halin damuwa. Wanda ya kai ni ga satar jariri" in ji Bunmi
Tun da farko dai lamarin ya faru ne a yankin Modakeke, da keJihar Osun, inda matar ta sace jaririn mai suna David Oluwaseun dan kimanin sati uku da hauhuwa.
Matar wacce ta ke mazauniyar karamar hukumar Magboro, Obafemi/Owode da ke jihar Ogun, an kamata ne a kauyen Orile na jihar Imo.
Da su ke gabatarwa manema labarai da ita, rundunar 'yan sanda ta kasa reshen jihar ta Ogun, karkashin shugabancin kwamishinan yan sandan jihar Ahmed Iliyasu ya bayyana matar ta dauki lamarin rashin haihuwa da matukar Zafi.
KU KARANTA: Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta
"Matar ta yi wa mijinta karyar tana dauke da juna biyu, inda bayan wata tara sai ta sanar da mijinta mai suna Adebayo cewa ta haihu, wanda hakan ya sanya shi farin ciki tare da garzayowa domin yin tozali da abin da aka haifa masa" in ji Ahmed Iliyasu.
Ya kara da cewa bayan zuwan mijin na ta ne, ya bukaci ganin mahaifar da ta ke zuwa bayan an haihu, amma sai hakan ya gagara. Daga nan sai ya bukaci da ta shayar da yaron a gabansa nan ma lamarin ya faskara.
Bayan da ta fahimci wannan al'amarin ya fusata mijin nata, sai ta gudu daga gidan, inda shi kuma ya yi gaggawar sanar da jami'an tsaro cewa matarsa ta bata. wannan ya sa 'yan sanda suka tsaurara bincike inda kuma su ka yi sa'ar gano ta a kauyen Orile da ke jihar Imo tare kuma da jaririn da ta sato.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng