Faduwar gaba asaran namiji: Shugaba Buhari ba zai hana kansa bacci akan wata jam’iyyar CUPP ba – Shugaban matasan APC

Faduwar gaba asaran namiji: Shugaba Buhari ba zai hana kansa bacci akan wata jam’iyyar CUPP ba – Shugaban matasan APC

Shugaban matasan jam’iyyar Progressives Congress (APC), Sadiq S. Abubakar ya yi watsi da jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP) da wadanda suka kafa ta, inda ya bayyana jam’iyyun siyasa 34 da suka hade a matsayin “jam’iyyar jakar hannu”.

“Wanene su? Sun kasance jam’iyyar siyasa na jakar hannu sannan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba katse baccinsa akansu ba,” Abubakar ya bayyana hakan a wata sanarwa day a fitar a Abuja a daren ranar Litinin.

Faduwar gaba asaran namiji: Shugaba Buhari ba zai hana kansa bacci akan wata jam’iyyar CUPP ba – Shugaban matasan APC

Faduwar gaba asaran namiji: Shugaba Buhari ba zai hana kansa bacci akan wata jam’iyyar CUPP ba – Shugaban matasan APC

Ya bayyana wadanda suka kafa jam’iyyar a matysayin wadanda suka fadi zabe, wadda suka kware wajen chanje chanjen jam’iyya.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal ya daura alhakkin kashe-kashe akan gazawar shugabanci

Shugaban matasan na APC yace masu hasashen cewa jam’iyyarsa zata fadi a zaben 2019 mafarki suke yi.

Yace yan Najeriya wayayyun ne babu wani da zai zo ya yaudare su ta hanyar chanja ma jam’iyya wacce ke cike da barayin yan siyasa suna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel