Kurame da bebaye sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnati
- Ba za ai mana danniya ba muna ji muna gani
- Masu bukata ta musamman sun nuna rashin amincewarsu da ci musu iyaka
- Sun gudanar da zanga-zangar ne a gidan gwamnatin Oyo
A Jiya ne wasu kurame da bebaye su ka yi wata zanga-zangar nuna kin amincewa da cin iyakar filin da aka yi musu, wanda aka kebe shi domin gina jami'a don masu bukata ta musamman da ke jihar Oyo.
Zanga-zangar wacce shugaban yan kwamitin amintattu Mr Silas Ike ya jagoranta ya bayyana cewa a 2004 aka sayi filin mai fadin murabba'in 39 akan hanyar Legas zuwa Ibadan da nufin gina jami'ar masu bukata ta musamman ta farko a fadin Afrika.
KU KARANTA: Abun dariya ne danganta ni da Saraki ga fashin Offa – Gwamnan jihar Kwara
Masu Zanga-zangar sun yiwa shelkwatar karamar hukumar Agodi tsinke, in da su ke dauke da kwalaye masu nuna rashin amincewarsu akan ci musu iyakar filin na su
A karshe kwamishina mai Lura da harkokin kasa da gidaje na jihar Oyo Mr Isaac Omedewu ya tabbatarwa da masu zanga-zangar cewa zai samu gwamnan jihar ta Oyo akan wannan al'amarin, kuma ya ce babu shakka za'a zauna da shugabancin kungiyar a mako mai zuwa.
A karshe shugaban masu zanga-zangar Silas Ike ya ce wannan matakin da kwamishinan ya dauka shi ne abin da ya dace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng