Abin murna Buhari ya samu jika: Zahra Buhari ta haifi namiji a kasar Spain
- Labari mai dadi ga 'yan Najeriya, domin sun samu jika
- 'Yar gidan shugaban kasa Buhari ta haihu a kasar Andalus
Kimanin watanni goma sha takwas da bikin yar gidan shugaban kasa Muhammad Buhari wato Zahra Buhari, wani rahoto da ya riske mu yanzu daga kafar sadarwa ta yanar gizo ta kikiotolu.com, ya bayyana cewa 'yar shugaban kasar ta haifi santalelen jaririnta cikin koshin Lafiya, a wani asibiti da ke kasar Spain.
Wata Majiya daga zuri'arta, sun bayyana yadda wannan haihuwa ya sanya farin ciki a tsakaninsu.
KU KARANTA: Ahmed Musa ya baiwa Sarkin Musulmi wata babbar kyauta (Hotuna)
Idan za'ai iya tunawa dai a cikin Shekarar 2016 ne, Zahra Buhari ta auri Ahmed Indimi dan gidan babban attajiri nan Alh. Mohammed Indimi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng