Fasinjoji 135 sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin saman Azman ya samu matsalar sauka a Kano
- Da sauran shan ruwan mutane sama da 135 a gaba, bayan da jirgin Azman ya fuskanci matsalar sauka
- Amma daga bisani an umarce shi da ya sauka a Abuja bayan da sauka a Kaduna ta gagara saboda rashin wutar lantarki
Sama da mutane 135 ne dake cikin jirgin saman Azaman kirar Boeing 737 ne suka tsallake rijiya da baya a jiya bayan da jirgin da yake dauke da su ya gagara sauka bayan yunkurin saukar har sau biyu a filin sauka da tsahin jirage na Mallam Aminu Kano (MAKIA) dake kano.
Jirgin dai ya taso ne daga filin sauka da tsahin jirage na Murtala Muhammad dake jihar Legas da karfe 11.30 pm na dare, kuma yayi yunkurin sauka ne a Kano da misalin 12.55a.m na dare amma yanayi maras kyau ya hana shi.
Wani ma’aikacin jirgin ya bayyana cewa tabbas rayuwar fasinjojin ta shiga farga. “Sauran kiris, kuma shallake rijiya da baya ne a lokaci guda, matukin jirgin yayi yunkurin sauka har sau biyu amma ya gagara, abu ne mai matukar hadari” ya shaida.
KU KARANTA: Yunkurin tsayawa takarar shugaban kasan Bukola Saraki ta haifar da rarrabuwar kai a R-APC
Wani daga cikin fasinjojin mai suna Nura Aminu ya shaidawa jaridar The Guardian cewa, da farko direban jirgin ya fada musu cewa akwai yanayi maras kyau na iska mai karfi da ake yi wanda hakan ya sanya ba zai iya sauka ba, amma yayi musu alkawari na yin duk yadda zai iya don su sauka.
Daga bisani kuma ya fada mana cewa an ba shi ikon sauka amma koda ya yunkura ya saukan sai ya sake fuskantar matsananciyar iskar. Aminu ya bayyana.
“Mun bata kamar mintuna 20 a sararin sama, to mai kake tunanin zai faru idan da bamu da isasshen mai?, Mun dai godewa Allah" (da ya sauke mu lafiya).
Daga baya dai an baiwa jirgen umarnin ya mika zuwa babban birnin tarayya Abuja, inda ya samu sauka a can da misalin karfe 2:00 am na dare. Bayan da yunkurin sauka a filin saukar jirage na jihar Kaduna ya ci tura bisa rashin wutar lantarki gaba daya a cikinta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng