Hukuncin kotun koli: Dogara ya taya Saraki murna

Hukuncin kotun koli: Dogara ya taya Saraki murna

Kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara ya taya shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki murnar nasarar da yayi a kotun koli a ranar Juma’a, 6 ga watan Yuli.

A wata sanarwa da Dogara ya fitar a ranar Juma’a a Abuja ta hannun mai ba shi shawara akan harkokin labarai, Mista Turaki Hassan, ya ce ya samu labarin hukuncin kotun koli cike da farin ciki.

Ya bayyana cewa hukuncin ya nuna amana a bangaren shari’a a lokacin da mutane basu yi tsammani ba.

Kakakin ya bayyana cewa bayan shekaru uku yanzu zukata zasu huta sannan kuma cewa duk da zarge-zarge gaskiya tayi halinta a karshe.

Hukuncin kotun koli: Dogara ya taya Saraki murna
Hukuncin kotun koli: Dogara ya taya Saraki murna

Dogara ya bukaci Saraki da ya kalli shari’an a matsayin jarrabawa ga shugabancinsa, sannan ya yi yafiya gami da barin kiomai ya wuce.

KU KARANTA KUMA: Ina da digiri a fannin hada magunguna da digiri na 2 a fannin tsarin lafiya amma na zabi aikin gyaran jiki domin dogaro da kai - Matashiya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kotum kolin Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, daga dukkan laifukan da kotun CCT da gwamnatin tarayya ke masa na rashin bayyana kadarorinsa.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar kotun daukaka kara da Jastis Centus Nweze ya yanke a yau Juma'a, 6 ga watan Yuli, 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng