Mutane 24 ke gadin Hajr-el-Aswad a Harami, shin me yasa?
Hajarul Aswad: Ma’anar wannan kalma a harshen Hausa shine ‘bakin dutse’. Wannan dutse na ajiye a gabashin jikin Ka’abah a harami. Ana daukn wannan dutse da matukar muhimmanci a addinin Musulunci. Shine dutsen da Allah ﷻ ya turowa manzo Ibrahim ﷺ daga sama.
Alakar annabi Ibrahim da Hajarul aswad: Allah ya umurci manzonsa Ibrahim ya sanya dutsen mai albarka a wani lungun Ka’aba. Daga bakin dutsen aka fara Tawafi kuma nan ake tsayawa.
Mahajjata da masu gabatar da Umrah na sumbatan dutsen a matsayin Ibadah saboda manzon Allah ﷺ da sahabbansa sun yi wannan abu.

Dutsen ya taba fashewa: A da, dutsen guda daya ne babba, amma bisa ga wasu rikice-rikicen tarihin da ya faru, an fasa dutsen zuwa balli 8. An tattara Wannan balli takwas cikin qwaryan azurfa domin hanashi sake fashewa.
A shekarar 930, mayakan Al-Karmati sun sace Hajarul Aswad, suka hallaka jama’a a harami kuma suka jefa gawawwakinsu cikin rijiyan Zam-Zam.
Sai a shekarar 952 ne aka samu daman dawo da Hajarul Aswad. Tun daga lokacin aka sanya masu gadi na musamman domin kula da dutsen a koda yaushe.
KU KARANTA: Wannan Amarya ta rasu a daren ranan aurenta
Jami’an tsaro 24 ke tsaron Hajarul Aswad a ranan daya. Kowanne daga cikinsu zai tsaya a wajen na tsawon sa’a daya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng