Ina da digiri a fannin hada magunguna da digiri na 2 a fannin tsarin lafiya amma na zabi aikin gyaran jiki domin dogaro da kai - Matashiya
Babu shakka matasan Najeriya na cigaba da bin shawarwari game da yadda mutum zai dogara da kanshi ba tare da jiran gwamnati ta sama masa aiki ba.
Labarin wata matashiya mai suna Amina zai tabbatar maka da hakan. Ta kasance mace mai kamar maza wacce ta jajirce wajen ganin ta tsaya da kafafunta.
Duk da cewar Amina ta yi ilimi mai zurfi bata tsaya cewar sai gwamnati ta sama mata aiki ba, ta dubi yanayin wajen da take zaune sannan tayi tunani mai zurfi don ganin abun da zai kawo ci a yankin.
Ga dan takaitaccen tarihin Amina a kasa:
"Sunana Amina Yakubu. Na karanci fannin hada magunguna a jami’ar Maiduguri sannan daga baya na yi digiri na biyu fannin tsara lafiya.
KU KARANTA KUMA: Hadimin Buhari ya gargadi dan majalisar wakilai kan kiran shugaban Najeriya da ya yi da azzalumi
“Na zabi zama ‘yar kasuwa saboda sha’awar abun. Yanzu haka ina dad akin kyaran kai da wajen siyar da kayayyakin sawa. Duk inda ka je akwai mata, sannan suna nukatar wajen gyaran jiki. Mata na son ado da kwaliyya. Don haka muna yin wannan harka, muna gyaran jiki, gashi da kuma fuska.
“Ina farin cikin ganin mata sun zo wajenmu suna neman taimakonmu sannan su bar wajen gyaran gashin cikin farin ciki. Hakan ya fi mani komai. A kullun ina mafarkin ganin na mallaki wajen gyaran jiki.
“Mutane na ganin na bar fannin da na karanta amma har yanzu ina ba marasa lafiya shawarwari sannan kuma na daura su akan magani.
“Daga baya ina son mallakar dakin hada maguguna. Ba zan damu ba ace ina da dakin hana magunguna da na gyaran jiki kusa da juna. Duk hakan burina ne.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng