An gurfanar da dan shekara 70 da ya lalata yar shekara 16

An gurfanar da dan shekara 70 da ya lalata yar shekara 16

Kayode Oshakoya, dan shekara 70 da aka zarga da lalata yarinya yar shekara 16 zai shafe kwanaki 25 masu zuwa a gidan yari, kamar yadda wata kotun majistare dake Ikeja ta yanke a ranar Alhamis a jihar Lagas.

An gurfanar da Mista Oshakoya a kurkukun Kirikiri zuwa ranar da za’a ji shawarar shugaban hukumar mahukunta na jiha (DPP).

Shugaban kotun na majistare, P. E. Nwaka, ya yi umurni kan a mika takardun shari’an zuwa hukumar DPP don jin shawararsu.

Wanda ake zargi, dake zaune a gida mai lamba 25, Ibrayumu St., Bariga, Lagos, ya aikata laifin fyade ne.

An gurfanar da dan shekara 70 da ya lalata yar shekara 16
An gurfanar da dan shekara 70 da ya lalata yar shekara 16
Asali: UGC

Da farko, dan sanda mai kara, Christopher John, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuni a gidansa.

Mista John ya bayyana cewa yarinyar ta je ziyara ga wanda ake zargin, wanda ya kasance abokin ahlin gidan, cewa da ta kai gidan sai ya yi mata fyade.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Najeriya za ta fara jigilar alhazai zuwa kasar Saudiya a ranar 21 ga watan Yuli

Ya bayyana cewa yarinyar ta fadama mahaifinta dukka abunda Mista Oshakoya yayi mata a lokacin day a dawo daga aiki.

An sanya ranar 30 ga watan Yuli domin cigaba da sauraron shari’an.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng