Fadar Shugaban kasa ba ta da wasaniya akan hukuncin da aka bayar na tsige Shugaba Buhari - Lai Mohammed
- Maganar tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama jita-jita
- Ministan yada labarai na kasa ne ya shaida hakan
- Tun farko dai kotu ce ta amshi korafin wasu lauyoyi na son su fara shirin tsige shugaban kasar a cikin makon da muke ciki
Ministan yada labarai da al'adu na kasa Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da masaniya akan hukuncin da wata kotu ta yanke na baiwa majalisar dokoki ta kasa umarnin fara shirye-shiryen tsige shugaban kasa Muhammad Buhari .
Ministan yada labaran ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, jim kadan da kammala zaman majalisar zartarwa na kasa wanda ya gudana a jiya larabar.
Tun da farko dai wata babbar kotu ce ta amince da bukatar da wasu lauyoyi suka shigar na bai wa majalisar dokokin kasar umarnin tsige shugaba Muhammadu Buhari.
KU KARANTA: Za'a kwashi ilimi: Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya
Alkalin babbar kotun da ke garin Osogbo jihar Osun, mai shari'a Onyetenu ce ta bayar da umarnin a ranar laraba, bayan da wani lauya mai suna Kanmi Ajibola da Sulaiman Adeniyi wani dan rajin kare hakkin dan Adam suka bukaci kotun ta dauki wannan matakin.
A karshe Ministan ya ce shi ma labarin ya zo masa a matsayin jita-jita, Sabo da haka akwai bukatar ya karanta hukuncin kafin ya tofa albarkacin bakin sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng