Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na yunkurin bincike a kudin satan Abacha da aka dawo da su daga 1998 zuwa yanzu
A ranar Laraba, 4 ga watan Yuli, mambobin majalisar wakilai sun yanke shawarar kafa wata kwamiti don bincikar kudin da Janar Sani Abacha ya sata ya boye a waje wanda aka dawo da su tun daga 1998 zuwa yanzu.
A karshen binciken ana sa ran kwamitin zata tono duk wasu kudade da aka gano da kuma yanayin biyan kudin, yadda aka kashe kadaden sannan kuma sub a majalisa rahoto cikin makonni shida.
Wannan cigaban na daga cikin matakin da majalisar ke shirin dauka na hana kashe kudaden karshe na Abacha ba tare da amincewar majalisa ba.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewar za ta fara kashe kudaden da ta kwato daga cikin arzikin da tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya kai su kasashen waje daga watan gobe na Yuli.
KU KARANTA KUMA: Ka kashe kudin Abacha kan ayyukan da talakawa za su gani kuru-kuru da idanunsu – Shehu Sani ga Buhari
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnati ta ce zata kashe kudaden ne ta hanyar yi ma yan kasa hidima, kamar yadda mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tallafa ma jama’a, Maryam Uwais ta bayyana a ranar Alhamis,28 ga watan Yuni.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng