Obaseki, Okonjo-Iweala sun nuna goyon bayansu ga yaki da cin hanci da rashawa

Obaseki, Okonjo-Iweala sun nuna goyon bayansu ga yaki da cin hanci da rashawa

Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki da tsohuwar ministar tattalin arziki, Misis Ngozi Okonjo-Iweala sun bukaci yan Najeriya da su marawa kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhar wajen ganin an magance matsalar cin hanci da rashawa daga kasar.

A wata hira daban-daban da suka yi bayan kammala taron shugabannin kasashen Afrika wanda aka kammala a Mauritaniya, mai taken “Nasara wajen yaki da rasawa, hanyar sabonta Afrika,’ Gwamna Obaseki da tsohuwar ministan kudin sun bukaci yan Najeriya da su marawa yaki da rashawar shugaba Buhari baya domin ingancin Najeriya.

A cewar Obaseki, “nahiyar Afrika bata fitar da rai akan mu ba saboda suna ganin shugabanmu a matsayin mutum dake son ganin bayan wannan matsala, wanda muke fama das hi a matsayinmu na kasa don haka ina son yan Najeriya su fahimci cewa yakin ba wai na son zuciya bane.”

Obaseki, Okonjo-Iweala sun nuna goyon bayansu ga yaki da cin hanci da rashawa
Obaseki, Okonjo-Iweala sun nuna goyon bayansu ga yaki da cin hanci da rashawa

A nata bangareb Okonjo Iweala ta ce: “Mun kasance a taron kungiyar Afrika saboda AU ta damu matuka akan cin hanci da rashawa a nahiyar Afrika. Aka yi dace, kungiyar ta bukaci shugaban kasarmu da ya jagoranci yaki da rashawan. Abun da hakan ke nufi a ganina shine cewa a Najeriya akwai mukatar mu karfafa kokarinmu, muyi aiki sosai don tabbatar da cewa mun kafa tarihi.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole Buhari ya yi murabus idan har ba zai iya dakatar da kashe-kashe ba – Manyan limaman coci

“Ina ganin ya kamata ace anyi wannan tafiya da dukkaninmu. Zan maimaita cewa yaki da rashawa babban aiki ne a gaban ko wani dan Najeriya. Nayi ammana da cewa mafi akasarin yan Najeriya masu gaskiya ne, sannan kuma mutane ne masu kwazo dake son ganin cigaban rayuwarsu.

"Don haka kada mu bari yan tsiraru su sha kan mutane masu rinjaye. Dole mu yake su, dole mu gyara lamarin hakan kuma zai yiwu ne da taimakon kowa."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel