Nigerian news All categories All tags
Mahaifi na ne ya fara kwanciya da ni tun ina ‘yar shekara 8 a Duniya - Wata yarinya

Mahaifi na ne ya fara kwanciya da ni tun ina ‘yar shekara 8 a Duniya - Wata yarinya

- Wannan lalacewa har ina, wata yarinya ta bayyana yadda ubanta yayi mata fyade

- Bayan fyaden kuma yayi mata auren dole ga wanda ko sadaki bai biya ba

- Amma sai dai duk sun shiga hannun hukuma

Wata yarinya mai kimanin shekaru 14 mazauniyar unguwar Ketu Epe a jihar Lagos, ta bayyana yadda mahaifinta Olawale Ibitoye ya ke kwanciya da ita tun tana 'yar shekara 8, a karshe kuma ya tursasata yin aure wanda hakan ya kawo mata cikas na cimma burinta.

Mahaifina ya yara kwanciya da ni tun ina ‘yar shekara 8 a Duniya

Mahaifina ya yara kwanciya da ni tun ina ‘yar shekara 8 a Duniya

Yarinyar ta bayyana hakan ne a bainar jama'a lokacin da ta ke cikin wata doguwar nakuda, wanda hakan ya yi sanadiyar haihuwar jaririya amma ba ta zo da rai ba.

Wanda hakan ya sanya rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Lagos din suka damke Mahaifin yarinyar bisa wannan danyen aikin da ya aikata.

Kwamishinan yan sandan jihar Lagos Imohimi Edgal, ya yi karin haske dangane da yadda su ka kai ga nasarar damke Ibitoye.

"Al'amarin ya fito ne bayan da yarinyar ta dade tana nakuda, wanda ta yi kwanaki ba ta haihu ba, hakan ya sanya aka garzaya da ita gurin wani mai Maganin gargajiya, inda ita kuma ta tabbatar da cewa lallai mahaifinta ya taba saduwa da ita, sannan ya tursasa ta yin auren dole da wani mai suna Moses Okurukpe" in ji kwamishinan yan sandan na jihar Lagos.

Ya kara da cewa wannan auren wuri ne, Kuma cin zarafi ne.

KU KARANTA: An kama wata babbar jigo a APC tana safarar mata zuwa turai

A nasa bangaren mahaifin yarinyar ya musanta wannan zargin, inda ya bayyana cewa shi dai kawai abin da ya sani shi ne "Yarinyar ta gudu daga gida ne, tun daga nan bai sake ganinta ba sai da ciki tare da gabatar da wani mutum a matsayin mijin da ya yi Mata cikin.

ya kuma ce 'yar tasa ta daina makaranta tun tana aji hudun sakandire, bayan nan ne kuma ya sanya ta a wata cibiyar koyon dinki.

Shi ma Moses Okurukpe wanda shi ne mijin yarinyar wanda bayan kasancewarsa manomi kuma yana sana'ar kabu-kabu, ya bayyana cewa bai san matarsa tasa Raliat shekararta 13 a lokacin ba, sannan ya ce mahaifinta ya karbi kudi Naira 5,000 daga hannunsa a matsayin kudin da ya yiwa 'yar tasa rijista a makarantar koyon dinki.

"Ban biya sadakin Raliat ba, amma Ina daukar dawainiyarta, kuma ina ba ta Naira 500 kullum. Amma duk da haka ta ci amanata domin kuwa tana bin maza duk da kasancewarta mai dauke da juna biyu" inji Moses.

Kawo yanzu dai wadanda ake zargin da Laifin suna tsare a gurin yan sanda, inda ake gudanar da bincike, kuma da zarar an kamlla za'a gurfanar da su a gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel