Shugaba Buhari ya fara rabon kudaden sata - Fashola
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fara rabon kudaden da aka kama daga barayi karkashin kasafin kudin 2018.
Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola ya bayyana hakan a taron darasin tunawa da Herbert Macaulay a jami'ar Najeriya, Nsukka, a jiya.
Fashola ya ce shugaban kasar ya amince da naira biliyan 120 daga kudaden domin gyara hanyoyi a jihohi 36 a fadin kasar.
Ya kuma bayyana cewa ma'aikatar ta bayar da kwangilar gyara hanyoyi a jami'un tarayya 14, ciki harda UNN sannan za'a aiwatar da shirin binciken wuta a jami'un tarayya 37.
A halin da kae ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe da ake yi a kasar kan gurbatattun yan siyasa.
KU KARANTA KUMA: Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi
Ya ce yan siyasan dake aikata hakan sun kasance wadanda suka daina samun hanyar da za su saci dukiyar kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng