Labari mai dadi: An soma samar da tashar jirgin ruwa a yankin Arewa
Rahotanni sun kawo cewa, ma’aikata sun fara aikin jawo ruwan teku zuwa jihar Niger saboda samarwa da yankin arewacin kasar babban tashar jiragen ruwa.
Wannan aiki na tafiya ne akan umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma idan an kammala aikin sama da mutane miliyan biyu ne za su sami guraben aiki a gurin.
Manyan kaya daga sassa daban-daban na duniya za su ke shigowa Arewacin Nijeriya cikin sauki kamar yadda suke shigowa Kotono dake jamhuriyar Benin ko jihar Lagas.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Kotu ta hana Dasuki bukatar da ya nema na a biya shi N5bn na barnar da aka yi masa
A wani lamari na daban, Mun samu labari cewa a shekarar nan Kotun da aka kafa na musamman a zamanin Gwamnatin Buhari sun yanke hukunci fiye da 300 a cikin rabin shekara. Bayan nan kuma an dage wasu shari’an zuwa gaba.
Majalisar shari’a ta kasar watau NJC ta bayyana cewa Kotun da aka kafa sun zauna game da shari’a har 324 a cikin watanni 6.
NJC tace ta kuma yi watsi da shari’a 12 ban da kuma wasu shari’a 62 da aka daga zuwa wani lokaci.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng