Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

Yanzu Yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

A ranar Litinin, 2 ga watan Yuli ne aka rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Audu Sule Katagum.

Hakan ya biyo bayan tattace tare da tabbatar da shi da majalisar dokokin jihar Bauchi tayi a ranar Juma’an da ya gabata.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a babban dakin wasanni na Bauchi inda Khadi Dahiru Abubakar Ningi, ya ratsar da shi a madadin babban shari’a na jihar Justis Rabi Talatu Umar.

Yanzu Yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

Yanzu Yanzu: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Katagum

Justis Talatu ta yi wani tafiyan aiki Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya

Da yake jawabin godiya, Katagum ya yi alkawarin yin aiki tare da ba gwamnati cikakken hadin kai da kuma tabbatar da cewar an mulka mutanen bisa dimokradiyya a yar ragowar lokacin day a rage masu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel