Yanzu-yanzu: Yan sanda suna zanga-zanga a Maiduguri

Yanzu-yanzu: Yan sanda suna zanga-zanga a Maiduguri

Rikici ya barke a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno yayinda jami’an yan sanda da aka tura jihar suka gudanar da zanga-znaga ta hanyar tare manyan hanyoyi saboda rashin biyansu alawus dinsu na watanni 6.

Jami’an yan sanda sunce an tura su jihar Borno ne daga jihohi daban-daban domin taimakawa wajen yaki da rashawa.

Bisa ga abinda ya bayyana dai jami’an yan sandan sun fusata a yau Litinin inda suka fara harbe-harben bindiga sama wanda kuma ya tsorotar da mazauna.

Daya daga cikin jami’an yan sandan wanda aka sakaye sunansa ya bayyanawa jaridar Premium Times cewa “ Ba zamu yarda da haka ba; sama da watanni shida yanzu kenan babu alawus, babu wajen zama; bakin kofofin mutane muke yi, wannan abu ya isa.”

Kwamishanan yan sandan jihar Borno, Damian Chukwu, wanda yayi magana da manema labarai a waya y ace hukumar yan sanda na sane da wannan abu. Ya yi bayanin cewa abinda ya sabbaba hakan shine rashin tabbatar da kasafin kudin 2018 da wuri.

Mr Chukwu ya ce jihar Borno ce gari mafi yawan jami’an yan sanda da ak tura.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng