An kama wata babbar jigo a APC tana safarar mata zuwa turai
- Ana zaton wuta a makera sai ga ta kwatsam a tsakiyar masaka
- Wata mai shirin zama 'yar siyasa ce ta shiga hannu bayan aikata wani babban laifi
- Kuma tuni har an gurfanar da ita gaban kotu tana shirin girbar abinda ta shuka
Yanzu haka dai an gano cewa wata ma’aikaciyar jinya ‘yar Najeriya mazauniyar kasar Ingila mai suna Josephine Iyamu, da wata kotu ta yankewa hukunci a can turai cewa ‘yar siyasa ce kuma babbar jigo a jam’iyya mai mulki ta APC, da tayi shirin tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.
Rahotanni dai sun bayyana cewa Iyamu na shirin tsayawa takarar majalisar jihar ta Edo daga karamar hukumar Egor. kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
Amma sai dai tayi rashin nasara a zaben fidda gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar.
wata kotu a Ingila ta samu Iyamu da laifin safarar mata biyar zuwa kasar Jamani domin aikata karuwanci.
Kuma za’a yanke mana hukunci ranar Laraba mai zuwa.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna
Wani abin mamaki dangane da ‘yar siyasar mai safarar matan shi ne, yadda take amfani da taken tallafawa mata da iyalai a matsayin abinda zata fi mayar da hankali mutukar aka zabe ta.
Yayin gudanar da shari’ar, an dai bayyanawa masu yanke hukuncin cewa ma’aikaciyar jinyar mai shekaru 51 ta umarci dukkan ‘yan matan da ta kawo daga kasar Najeriyar su saba rantsuwar boye sirrinsu da kuma alkawarin biyanta. A cikin wani yanayi mai kama da rantsuwar tsafi.
Daga cikin yanayin tsafin ya kunshi cin zuciyar Kaza da shan jini a cikin wata tasa cike da tsutsotsi da kuma barbadawa wani nama hoda.
Iyamu ta shiga hannu ne yayin wani sumamen da sashin masu yaki da safarar mutane (JBTF), tare da hukumar dakile laifuka ta kasar Birtaniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng