Tsugunno bai kare ba, barayin shanu sun yi kisa sannan su kayi awon gaba da shanu a Filato
- Barayin shanu sun sake tafka barna a Filato
- Bayan kashe wani dan banga sun tsere da shanunsa
- Wannan ta sanya wasu ke ganin akwai bukatar sauya fasalin yadda tsami'an tsario ke aiki
Salwantar rayuka sakamakon rikice-rikice a jihar plateau na cikagaba da afkuwa bayan kashe wani dan Banga mai kiwon shanu da wasu wadanda ake zargin makiyaye ne tare kuma da sace shanunsa guda tara wanda mallakin wani babban Malamin Cocin Angalikan ne mai suna Benjamin Kwashe.
Kakakin rundunar 'yansanda na Kasa reshen jihar Plateau Terna Tyopev , ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a jiya Asabar a kauyen Kangam dake yankin karamar hukumar Jos ta Kudu.
Ya kara da cewa kawo Yanzu dai an kai gawar Marigayin asibitin Jami'ar Bingham dake Jos, inda kuma Ya tabbatar da cewa tuni jami'an 'yansanda suka fara bincike akan faruwar al'amari.
Idan za'a iya tunawa dai ko a ranar lahadin da ta gabata an samu kai hare-hare wanda ake zargin makiyaya ne suka kai garuruwan Barkin-Ladi da Riyom da suke yankin Jos ta Kudu, wanda ya janyo asarar rayukan al'ummar wannan yanki fiye da 86.
Jim kadan da kai wancan harin da aka sace shanun ne 'yan Kabilar Berom dake jihar ta Plateau suka bukaci da a karbo musu kauyukansu Kimanin guda 52 wanda su ke zargin ya koma karkashin makiyaya.
KU KARANTA: Burina na gina coci-Inji wani shugaban yan fashi da makami bayan da ya shiga hannun hukuma
Wannan bukata dai ta fito ne daga bakin wata kungiya mai rajin tabbatar da cigaban 'yan asalin jihar Filato mai suna PIDAN wacce hadakace ta kabilu ‘yan asalin jihar ta Filato.
Inda su ka kara yin kira ga gwamanatin tarayya kan ta kara kokari wajen ganin ta binciko wadanda su ka kai wannan hari, domin a hukunta wadanda suka aikata wannan aikin.
Shugaban Kungiyar ta PIDAN Dr. Aboi Madaki ya bayyanawa manema labarai cewa mutane 22 da suka gudu daga kauyukansu sun fito ne daga karamar hukumar Barikin Ladi, yayin da 18 suka fito daga karamar hukumar Riyom sai kuma mutane bakwai daga karamar hukumar Bokkos ragowar mutane biyar din kuma sun fito ne daga karamar hukumar Bassa.
A karshe ya yi Kira akan sake fasalin tsarin dokar tsaro, domin hakan ne kadai zai baiwa jami'an tsaron damar daukar matakin magance matsalar masu kai hare-hare, ba tare da jiran umarni daga fadar shugaban kasa ba.
Sannan kuma ya bukaci gwamnati ta kaddamar da wani bincike akan Makiyayan domin ganin an kame dukkanin wanda da aka samu da makami.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng