Yanzu-yanzu: Buhari ya tafi kasar Mauritania
- Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Mauritania
- Zai yi kwana biyu a taron inda zai gabatar da jawabi
Labarin da ke shigowa yanzu na nuna cewa jirgin shugaba Muhammadu Buhari ya tashi yanzu a babban filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua da ke jihar Katsina zua kasar Mauritania domin halartan taron gamayyar kasashen Afrika wato AU na 31 ranan 1 da 2 ga watan Yuli, 2018.
Taron na wannan shekaran dai na ke take : “Samun nasara kan yaki da rashawa: Yadda za’a kawo sauyi nahiyar Afrika”. Shugaba Muhammadu Buhari ne zai gabatar da jawabi na musamman akan wannan take.
Sannan shugaban gamayyar kasashen Afrikan kuma shugaban kasan Ruwanda, Paul Kagama, zai gabatar da jawabi kan sauye-sauyen gamayyar, shi kuma shugaban kasan Nijar, Mahamadou Issoufou, zai gabatar da nasa kan kasuwanci a Afirka.
Wannan shi ne karo na farko da za’a yi taron a kasar Mauritania tun bayan kafa ta.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng