Ku bani dama ku gani idan ban kora Buhari gida ba – Baba Ahmed
Dan takarar shugabancin kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Datti Baba-Ahmed, ya fada ma jam’iyyar cewa su bashi tikitin takarar shugabancin kasa, cewa zai kora shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a zaben shekara mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne sakatariyar jam’iyar ta kasa dake Abuja lokacin da ya je kaddamar da kudirinsa na tsayawa takara a ranar Juma’a.
Da yake gabatar da kansa a matsayin wanda ya zuba jari wajen cigaban matasa ta hanyar ilimi, dan takarar wanda ya kasance jagoran jami’ar Baze, Abuja ya ce duk da cewar bai samu tikitin ba, zai ci gaba da ba jam’iyyar hadin kai.
Ya ce yaki da rashawan gwamnati mai mulki shirme ne domin a cewarsa ta hanyar rashawa aka kawo gwamnatin mulki.
KU KARANTA KUMA: Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari
Ya ce shugaban kasar ba zai iya cewa shi baya rashawa alhalin ya mamaye kansa da yan uwa da abokanai wadanda suka zamo masu arziki a gwamnati.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng