Da duminsa: Bayan Sallar Juma'a a Katsina, Buhari ya isa gida Daura

Da duminsa: Bayan Sallar Juma'a a Katsina, Buhari ya isa gida Daura

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa mahaifarsa Daura, jihar Katsina cikin wani kyakkyawan tarba da al'ummar garin sukayi masa a ziyara da ya kawo.

Legit.ng Hausa na baku rahoton cewa jirgin mai saukan angulu da shugaban kasan ya dira a garin Daura ne misalin karfe 3:15 na ranan bayan Sallatar Juma'a a Katsina tare wasu yan'uwansa na jini.

Masoya, abokan arziki, yan'uwa da a;'ummar garin sun cika dam domin tarbarsa cikin wakoki masu yabonsa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Daga bayan ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin Daura, Mai Martana, Farouk Umar, tare da wasu mukarrabansa da yan siyasa.

Da duminsa: Bayan Sallar Juma'a a Katsina, Buhari ya isa gida Daura
Da duminsa: Bayan Sallar Juma'a a Katsina, Buhari ya isa gida Daura

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban Muhammadu Buhari ya isa jiharsa, jihar Katsina a yau Juma’a, 29 ga watan Yuni 2018 domin gaisuwan jaje ga wadanda annobar ambaliyar ruwa ya shafa a watan Mayu.

Wannan ambaliyar ya tafka mumunan asara ga jama'a da inda ya hallaka muhallai akalla 53.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng