Yanzu Yanzu: Bayan fashewar Tanka, wani hatsarin ya sake faruwa a gadar Otedola
Kasa da sa’o’i 24 da afkuwar hatsarin motar tanka dake cike da mai wanda yayi sanadiyan konewar motoci 54 da kuma rasa rayukan mutane tara a gadar Otedola dake babban titin Lagas zuwa Ibadan, an kuma yin wani hatsari a dayan bangaren da hatsarin ya faru.
Rahoton dake isar mana ya nuna cewa wani direban motar haya ta Danfo ne ya kara da wata motar Toyota Hiace bayan yayi kokarin bin barauniyar hanya guda.
An tattaro cewa direban na tuki da gudu ba bisa ka’ida ba.
An dauki wadanda suka samu ranu sanadin wutan ya tashi zuwa asibiti haka zalika an dauke motocin daga hanya.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Kashe-kashe: Gwamnoni sun kai ziyarar jaje jihar Plateau
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng