Hotunan kyakkyawan tarban da Buhari ya samu yau a Katsina
Shugaban Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Katsina yau Juma’a, 29 ga watan Yuni domin jajintawa wadanda annoban ruwan sama ya shafa da iyalansu.
Shugaban kasan ya samu samu kyakkayawan tarba ne daga gwamnan jihar, Mal Aminu Bello Masari, manyan jami’an gwamnatin jihar, da kuma alummar jihar da suka tasaya kan titi domin ganin wucewansa.
Daga bisani shgaba Buhari ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Usman, inda ya mika sakon jajensa sarkin kan ambaliyar da ya hallaka al’ummar garin da kuma lalata muhallansu a watan Mayu.
Kalli jerin hotunan yadda jama’ar garin suka tarbesa;
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng