Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari

Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari

A ranar Juma’a, 29 ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cewa zai goyi bayan duk wani yunkuri da zai kawo inganci ga lamarin tsaro a nahira Afrika ta Kudu.

A cewar wata sanarwa daga hadiminsa, Femi Adesina, shugaban kasar yayi Magana ne yayinda ya amshi bakuncin shugaban kungiyar kasashen Afrika kuma shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe, a Katsina.

Buhari yace a yanzu yan ta’adda na addaban iyakokin kasashe, sannan kuma cewa babu kasar da zata iya wannan yaki ita kadai.

Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari
Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari

Buhari ya kuma yabawa bukatar da aka gabatar na yin wani taro na tsaro tsakanin mambobin ECOWAS da na kasasashe dake yankin Afrika ta tsakiya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tirela ya yi karo da tankar mai a hanyar Suleja-Minna

Za’ayi taron tsaron ne a ranar 30 ga watan Yulin wannan shekarar.

Gnassingbe ya ce yayi farin cikin kasance a Katsina, mahaifar shugabna kasar, sannan ya yi godiya ga mai masaukin bakinsa kan taimakawa da yayi wajen daidaita lamarin siyasa a Togo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel