Rasha 2018: Azumi ne ya hana 'yan wasanmu nasara — Masar

Rasha 2018: Azumi ne ya hana 'yan wasanmu nasara — Masar

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Masar ya ce fadowar azumi dab da lokacin gasar cin kofin duniya ne ya shafi rawar ganin da tawagar kasar ta shirya wa gasar da ake yi a kasar Rasha.

'Yan wasan sun zabi suyi azumin Ramadana duk da lokacin dake tsakanin wasansu na farko da kammala azumin ba mai tazara ba ne.

Kasar Masar, da ta buga da Uruguy da Rasha da kuma Saudiyya, ta fadi a duk wasannin inda ta zo ta karshe a rukuninta na A.

Rasha 2018: Azumi ne ya hana 'yan wasanmu nasara — Masar
Rasha 2018: Azumi ne ya hana 'yan wasanmu nasara — Masar

Kuma ya kara da cewa yana mai tabbatar da cewa kasashen Larabawa da yawa sun sa 'yan wasansu sun sha azumi.

KU KARANTA KUMA: Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasar Chechnya Ramzan Kadyrov ya girmama dan wasan kwallon kafar Egypt kuma mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wasa da takardar zama cikakken dan kasar.

Hakan ya faru ne a wani taro da aka gudanar na bankwana da kasar Russua kasancewar an cire su a gasar cin kofin duniya.

Ƙasar Masar ta zaɓi tana atisaye a ƙasar Chechenya kasancewar tan makwabtaka da kasar Russia ta daf da daf daga ɓangaren kudanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng