Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa

Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa

- Da alama jam'iyyar APC bata ji dadin ayyan kwanaki bakwai na hutun jimami a kasa baki daya da PDP tayi ba

A dalilin hakan ne ma APC ta mayarwa da PDP wani martani mai kama da tashin liki

- 'Yan adawa musamman daga jam'iyyar PDP na gani gazawar gwamnatin APC wajen yin katabus akan lamarin

Fadar shugaban kasa ta ga baiken babbar jam’iyyar adawa ta PDP bisa amfani da halin kashe-kashen da yake faruwa a Filato suna makokin gangan da kuma nuna alhinin karya, a cewar fadar shugaban kasar irin hakan ba komai ba ne face neman goyon baya a lokacin alhini.

Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa
Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa

A cikin jawabin fadar shugaban kasar sun zayyano irin rikice-rikicen da suka faru tun daga lokacin da jam’iyya ta fara mulkin kasar nan daga shekara 1999 kafin faduwa a hannun jam’iyyar APC a shekarar 2015.

“Abin takaici ya afku a jihar Filato karshen makon da ya gabata, amma sai dai kash ‘yan adawa sun kara siyasantar da lamarin musamman jam’iyyar PDP da har tsunduma cikin zaman makokin kwanaki 7.

Wannan lokaci ne na bakin ciki da damuwa bisa yadda aka mayar da rayuwar mutane ba a bakin komai ba, sannan kowa ya bayar da shawarar yadda za’a magance matsalar, amma PDP ta mayar da hankali wajen sanya siyasa ciki, wanda hakan abin tir ne".

Jam’iyya PDP dai ta bayar da umarnin sauke tutar jam’iyyar kasa a dukkan ofishinta na tsawon kwana biyu domin nuna jimami ga kashe-kashen da ya afku a jihar Filato, sai dai wani abu da PDP bata sani ba shi ne tutar tasu ta dade a kasa tun bayan da suka fadi zaben 2015 kuma zata ci gaba da kasancewa a hakan har nan da lokaci mai tsawo.

KU KARANTA: Ana zargin APC da kashe sama da Biliyan 3.6 wajen gangamin Jam’iyyar

Don kuwa ‘yan Najeriya tuni kansu ya waye sun kara wayo a siyasance kuma ba zasu yarda a sake yi musu shigo-shigo ba zurfi ba, a cewar jam’iyyar APC.

Daga nan ne jam’iyyar APC ta zayyano irin kashe-kashen da a kayi a lokacin PDP na mulki tun daga 1999 zuwa 2015 amma bata shiga zaman makoki ba.

-Ranar 20 ga watan Nuwamba 1999, a garin Odi dake jihar Bayelsa, an yiwa garin dirar mikiya bisa umarnin shugaban kasa dan jamiyyar PDP inda mutane kusan 2,500 suka sheka barzahu. Amma ba suyi zaman makoki ba.

-Tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayun 2000 kusan mutane 5,000 ne suka gamu da ajalinsu yayin da akayi wata zanga-zanga don kaddamar da shari’ar musulunci a jihohi da dama na arewacin Najeriya. Amma ba suyi zaman makoki ba.

-A shekarar 2001 daruruwan mutane ne da suka hada da tsofaffi da mata har da ma yara kanana aka karkashe su a garin Zaki Biam. Amma ba suyi zaman makoki ba.

-Tsakanin watan Satumba 7-12-2001 a garin Jos jihar Filato, wani rikici ya barke nan ma mutane tsakanin 500 zuwa 1,000 ne suka garzaya lahira. Amma ba’a ko karkata tutar PDP kasa ba.

-A cikin watan Fabrairu 2004 a kalla mutane 975 ne aka kashe su a Yelwan-Shendam cikin jihar Filato. Wannan ma babu labarin ranar jimami daga jam’iyyar PDP.

-A dai cikin jihar Filaton ranar 28 ga watan Nuwamba 2008 wani rikicin ya ja ragamar mutanen da yawansu ya kai 381, Amma ba suyi zaman makoki ba.

-A shekarar 2010 mutane 992 ne aka kashe a garin Jos amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

-Haka zalika a shekarar 2014 a wani kiyasi da aka fitar na alkalumman ta’addanci a duniya, ya nuna cewa a kalla mutane 1,229 ne suka mutu a yankin tsakiyar Najeriya (Middle Belt), nan ma babu wani jimami.

-‘Yan ta’addan Boko Haram kadai mutanen da suka kashe a lokacin da PDP take mulki sun kai 10,000, amma tutar PDP tana sama sai kadawa take cikin sararin sama cikin alfaharin zama a kujerar mulkin Najeriya.

A don haka sai a kula da masu caccanza mana zance wai muna cewa an fi kashe mutane a mulkin PDP kan na shugaban kasa Muhammadu Buhari, a’a wannan jawabi namu na nuni ne kawai kan yadda wannan mummunan hali na kashe-kashe ya dan jima a tare da mu wanda gwamnatin shugaba Buhari ke mutukar kokari wajen nemo mafita. Don haka sai a bata damar yin hakan.

Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa
Rikicin Filato: Gwamnatin tarayya ta mayarwa da PDP martani kan amfani da rikicin wajen cimma manufar siyasa

Rai ko da daya ne yana da mutukar muhimmanci, kuma babu wani mai ikon kashe sa domin ba zai iya halittarsa ba, amma idan wani abu makamancin abinda ya faru a garin Filato ya afku to bai kamata a siyasantar da shi ba. Masu yin hakan kuma ya kamata su canza ko kuma imaninsu da jin kansu ga bil Adam babu shi a jikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng