Wata mata ta bukaci kotu ta raba aurenta da maigidanta saboda rashin samun kulawa
- Fadan masoya hutu ne amma anan igiyar auren ce ma gaba daya ke shirin datsewa
- Kowa na zargin juna tsakanin ma'auratan
- Amma wani dalili guda tak yafi ci wa matar tuwo a kwarya
Wata 'yar kasuwa a jihar Legas ta roki kotu da ta raba aurenta da maigidanta bayan shafe shekaru 14 tare, hakan ya biyo bayan korafin da ta bayyana a gaban kotun na rashin samun kulawa musamman ta bangaren da ya shafi kwanciya ta ma'aurata.
Matar mai suna Monsurat Ogundipe da maigidan nata suna zaune ne a unguwar Ijaiye dake yankin Egba na jihar ta Legas, ta jadaddawa mai Shari'ar cewa ita sam bata bukatar cigaba da zama da maigidan nata.
Monsurat Ogundipe ta ce "Mijina ba mutum ne mai kamala ba, karya ta masa yawa ga rashin gaskiya, duk abinda zai fada ba gaskiya a cikinsa, kuma ya kasance yana zubar mana da mutunci ni da yarana saboda shan giyar da yake, kuma abinda ya fi damuna shi ne yanzu mun kai shekaru 2 kenan ba tare da yayi tarayyar aure dani ba".
KU KARANTA: Hanyoyi 5 da zaku bi don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa
"A rayuwar aurenmu bai taba duka na ba amma abu mafi muni da yake aikatawa su suka fi damuna. A lokuta da dama yakan kawo matan bariki har cikin gida ba tare da jin kunyata ba balle tsoron abinda yaransa zasu ce ba, gaba daya baya bawa aurenmu daraja ko kadan".
Shi daga bangaren wanda ake karar ya kuwa ya bayyanawa kotun cewa dama yana bukatar a raba auren nasu saboda shi ma a yanzu baya kaunar cigaba da zama da ita.
"Kamar yadda ta bayyana cewa ina neman matan banza ba gaskiya bane sharri ta min, kuma a matsayina na wanda suke karkashina ina iya bakin kokarina domin ganin na basu dukkan hakkinsu amma bata gode min.
Wannan al'amari ya samo asali ne tun bayan lokacin da wata 'yar uwata ta dawo gidanmu da zama daga wannan lokaci ne ta dauki karan tsana ta dora mata wai lallai sai ta bar gidan nima kuma ta daina ganin mutuncina har ta daina bani hakkina na zamantakewar aure wai har sai yar uwata ta bar gidan".
"Ni a yanzu babu wata sauran yarda tsakanina da ita dan haka ina rokon kotu da ta raba auren nan namu kowa ya kama gabansa" Mijin matar ya bayyanawa kotun.
Alkalin kotun Ibironke Elabor, ta shawarci ma'auratan da su sulhunta kan su kafin zaman kotun na gaba domin cigaba da sauraren shari'ar.
An saka ranar 26 ga watan Yuni domin cigaba shari'ar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng