Dan wasan gaba Ighalo ya nemi afuwar 'yan Nigeria kan wasan Argentina

Dan wasan gaba Ighalo ya nemi afuwar 'yan Nigeria kan wasan Argentina

- Rashin kokarin 'dan wasan Najeriya na daga cikin dalilin fitarta daga kofin duniya

- A don haka ne yake neman da a yafe masa kurensa

'Dan wasan gaban Najeriya Odion Ighalo ya bayyana rashin jin dadinsa tare da neman afuwa ga yan Najeriya, inda yace laifinsa ne na rashin amfani da damar da ya samu wajen zura kwallo a ragar Argentinar a lokacin da yake daga shi sai mai tsaron raga a yayin karawar Nigeria da kasar Argentina.

Dan wasan gaba Ighalo ya nemi afuwar 'yan Nigeria kan wasan Argentina
Dan wasan gaba Ighalo ya nemi afuwar 'yan Nigeria kan wasan Argentina

Ighalo dai ya canji dan wasan gaba Iheanacho ne saboda baya kokari amma shigowarsa bata sauya zani ba balle a samu biyan bukata.

KU KARANTA: Kofin duniya: Jami'an tsaro sunyi gargaɗi ayi hattara da harin ƴan ta'adda a gidajen kallon kwallo

Ighalo ya ce "Ina neman afuwa ga Najeriya da abokan wasana, saboda wannan rashin nasarar da muka laifina ne, saboda da na yi amfani da damar da muka samu da yanzu wani labari na daban ake yi ba wannan ba".

"Wannan rana ce mafi muni a tare dani saboda ya kamata ace mun yi nasara domin zuwa zagaye na gaba, amma babu abinda zamu yi face mu dauki dangana domin kwallon kafa ta gaji haka, wani lokacin zaka yi nasara wani lokacin kuma akasin haka".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng