Jiki da jini: Sarauniyar Ingila ba lafiya
- Sarauniya mafi dadewa a duniya na fama da rashin lafiya
- Har ta kai ta gazawa halartar taron da aka shirya gudanarwa yau
- Sanarwar rashin lafiyar nata na kunshe ne cikin wasikar da wanda ya wakilce ta ya bayar
A yau ne fadar sarauniyar Ingila ta sanar da cewa sarauniya Elizabeth II ba zata samu halartar taro na musamman da aka shirya gudanarwa yau a fadar St Paul’s Cathedral ba.
Sanarwar tana kunshe ne cikin wata wasikar da wanda aka aike a madadinta ya bayyana, "Sakamakon rashin jin dadin jikinta da sarauniya, ba zata samu damar halartar wannan bikin cikar wannan babban wajan bauta na St Paul’s Cathedral shekaru 200 da kafuwa ba."
Wanda ya wakilce ta a wurin taron, Prince Edward Sarkin Kent, ne ya bayyana hakan".
KU KARANTA:
Sarauniya Elizabeth dai ita ce sarauniya mafi dadewa a kan karagar mulki a fadin duniya, domin kuwa yanzu maganar da ake ta shafe kimanin shekaru 66 a gadon sarauta sannan ta kuma yi bikin murnar cikar shekarunta 92 a duniya a watan Afrilun da ya gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng