Jam’iyyar PDP ta jinjina ziyarar jaje da shugaba Buhari ya kai jihar Plateau
Babban jam’iyyar adawar Najeriya wato PDP ta jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ziyarar jaje da ya kai jihar Plateau ba tare da bata lokaci ba.
Kakakin jam’iyyar Shehu Yusuf Kura ya bayyana cewa wannan shine abun da ya dace ace shugaban kasa na yi. A cewarsa maimakon zuwa bude ayyuka a jihar Cross Rivers ta PDP da shugaban ya yi kamata ya yi a ci gaba da duba kalubalen tsaro a Zamfara, Birnin Gwari da wuraren dake fama da ayyukan ta’addanci.
Ya kuma bayyana cewa ba’a makara ba kuma suna fatan zuwansa zai sa a lalubo bakin zaren rigingimun.
Ya kamar yadda Buhari ya je jaje jihohin Bauchi da Plateau suna fatan duk inda aka samu tashin hankali zai daure ya je.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya isa jihar Plateau
Yayinda ake kashe mutane kullum a kasar Shehu Kura a madadin PDP na cewa ya makata gwamnati ta zauna ta shawo kan matsalolin idan da gaske take da samar da tsaro a duk fadin kasar.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara na cikin wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugabannin na ganawar ne akan kashe-kashe da aka yi a jihar Plateau a karshen makon da ya gabata. Shugabannin majalisar dokokin Najeriya ne suka bukaci yin ganawar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng