Neman duniya: Kato ya fito daga motarsa yana wanka zindir a bainar jama’a

Neman duniya: Kato ya fito daga motarsa yana wanka zindir a bainar jama’a

- An tuhumci wani dan Najeriya da aikin asiri yayinda aka ga yana wani abin da ya sabawa al’ada

- An kama shi yana wanka rana tsaka a wani tasha a jihar Legas

- Mazauna unguwan suna tambaya shin me ya sanyashi yin hakan

Wani abin mamaki ya faru a wani tashar jihar Legas yayinda aka ga wani mutum ya fito zigidir yana wanka da rana tsaka a bainar jama’a a jiha Legas.

Legit.ng ta tattaro cewa mutumin ya ajiye motarsa a gefe daya domin yayi wanka. An ganshi ta gefen motan yana wanka da soso da sabulu kuma yana watsa ruwa domin tsabtacce kansa.

Neman duniya: Kato ya fito daga motarsa yana wanka zindir a bainar jama’a
Neman duniya: Kato ya fito daga motarsa yana wanka zindir a bainar jama’a

Mazauna unguwar da suka ganshi suna tuhumarsa da yin hakan domin asirin neman duniya.

A wani bidiyo da aka daura a shafin Facebook, mazaunan suna kokarin hanashi wankan domin karya asirin da yake yi

Da farko kananan yara ne ke kallonshi a titi kafin manya suka iso wajen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel