Matasa a jihar Adamawa sun koma amfani da fitsari wajen bugewa - NDLEA
Hukumuar dakile ta’amuni da muggan kwayoyi wato NDLEA, shiya jihar Adamawa ta bayyana cewa wasu matasa a jihar Adamawa yanzu na amfani da fitsari wajen samun maye.
Kwamandan hukumar na jihar Adamawa, Kibo, ya bayyana hakan ne ranan Talata a jihar Adamawa a wani jawabi da ya gabatar domin murnan ranan yaki da safarar muggan kwayoyi na duniya a garin Yola.
Kibo yace wasu abubuwan da ake amfani da shi sune bushasshen ganyen gwanda, bushasshen ganyen ayaba, konannun tayoyi da kuma sanya Tom-tom cikin La casera.
A cewarsa: “Ya nada muhimmanci iyaye su sani kuma su mayar da hankali wajen sabbin abubuwan da aka gano ana amfani da shi irinsu bushasshen ganyen gwanda, bushasshen ganyen ayaba, konannun tayoyi da kuma sanya Tom-tom cikin La casera, zuba Spirit cikin Coca-cola, da kuma fitsarin da yayi kwanaki 10 a ajiye.”
Kibo yace wannan abun takaici bai bar kowa ba, ba yaran talakawa ba, ba na masu hannu da shuni ba. Hada karfi da karfe ne zai isa kawo karshen wannan abu.
KU KARANTA: Wata Shegiyar Uwa ta hallaka danta da wuta
Yace:”Daga watan Junairu zuwa yanzu, an damke kilon muggan kwayoyi 2,742.358 kg.”
Wadannan sun kunshi Ganyen Wiwi, Kwayar Tramol, Codeine, kwayan Diazepam, exol-5, da alluran pentozocine.
Yace wan damke dilolin wadannan kwayoyi 67 kuma an garkame 26 daga cikinsu a gidajen yari.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng