Nigerian news All categories All tags
Abin tausayi: Duba yadda wata uwa ta kwarawa danta kalanzir sannan ta cinna masa wuta

Abin tausayi: Duba yadda wata uwa ta kwarawa danta kalanzir sannan ta cinna masa wuta

- Zafin zuciya ya debi wata uwa ta hallaka danta da kanta

- Ta kashe dan nata ne ta hanyar babbaka shi kamar dabba

- Sai dai dama mahaifin yaron yace dama ya fara fuskantar sauyin halayya daga matar tasa

Obioma Odum yaro je dan shekaru 13 da haihuwa wanda ya gamu da ajalinsa bayan da mahaifiyarsa ta cinna masa wuta. Wannan lamari dai ya faru ne garin Umuahia dake jihar Abia.

Duniya ina zaki damu: Wata mahaifiya ta kwarawa danta kalanzir sannan ta cinna masa wuta

Duniya ina zaki damu: Wata mahaifiya ta kwarawa danta kalanzir sannan ta cinna masa wuta

Bayanai sun bayyana cewa mahaifiyar yaron mai suna Chinyere ta akaita hakan ne saboda yaron ya saci na'urar naɗe sauti da adana abubuwa wato (memory card) na wayarta sannan ta sa shi gaba tana ta duka daga bisani kuma zuciya ta debe ta har ta kwara masa kalanzir sannan ta bisa da ashana.

Wani wanda ya ganewa idonsa yadda abin ya faru ya bayyanawa manema labarai cewa, mahaifiyar yaron tare da kawarta wadda ba a bayyana sunanta ba sun daure yaron ne tare da saka shi a madafar abinci, inda suka zuba masa kalanzir domin tilasta shi ya bayyana inda ya kai abinda ya sata.

KU KARANTA: Rikicin jihar Plateau: An sanya dokar ta baci a jihar Plateau

Wanda ya gane wa idonsa yace "Matasa ne suka garzaya zuwa madafar abincin a yayin da suka hangi wani hayaki yana tashi bayan da suka bude sai suka same shi yana ci da wuta nan take aka tafi dashi zuwa asibiti wanda kafin aje har ya samu ƙunannaki guda 54 a sassan jikinsa".

"Lokacim da abun ya faru bana gida ina wajen aiki, sai naga kiran wayar dan uwana inda yake shaida min cewa ai ga matata nan da wata kawarta sun kona min yaro, kafin na karaso wasu matasa sun dauke shi zuwa asibitin jami'an yan sanda da yake kusa damu" .

"Daga baya aka tura mu zuwa asibitin FMC dake Umuahia, su ma sai suka bukaci da mu dawo washegari domin mu dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na jihar Enugu, amma kafin mu kai ga daukarsa rai yayi halinsa", Inji mahaifin yaron.

"Ni dai na kasance cikin rayuwar zaman lafiya da mai dakina tun a shekaru da suka gabata a baya, amma a baya-bayan nan duk ta bi ta canja halayenta saboda akwai wani rikici da muka taba samu har kaina ta fasa min da fartanya". Kamar yadda mahaifin yaron ya bayyanawa manema labarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel