Ma'aikatu 50 na Gwamnatin Tarayya da babu Jagorori

Ma'aikatu 50 na Gwamnatin Tarayya da babu Jagorori

Akwai kimanin ma'aikatu 50 na gwamnatin tarayya da masu rikon kwarya ki gudanar da al'amurran su bayan tsawon shekaru da shugabannin ma'aikatun suka yi murabus ko kuma aka sallama daga bakin aiki da hakan ya janyo tafiyar Hawainiya wajen gudanar da al'amurran ma'aikatun kamar yadda bincike na jaridar Daily Trust ya bayyana.

Hakan ya bayu ne bayan tsawon watanni takwas da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwa kara yawan Ministoci cikin majalisar sa da kuma sabbin nade-nade a wasu ma'aikatu na kasar nan.

A ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya bayyana kudirin sa na na fadada majalisar sa yayin zaman majalisar zantarwa inda zai kara adadin Ministocin sa daga 36 zuwa wani adadi da bai fayyace ba.

Hakazalika shugaban kasar ya bayyana cewa zai gudanar da sabbin nade-nade a wasu Ma'aikatu na kasar nan.

Ma'aikatu 50 na Gwamnatin Tarayya da babu Jagorori
Ma'aikatu 50 na Gwamnatin Tarayya da babu Jagorori

Akwai kimanin Ma'aikatu 12 da babu tsayayyen jagora dake karkashin Ma'aikatar ilimi, 11 a ma'aikatar noma, 3 a ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje, biyu karkashin ma'aikatar labarai da al'adau yayin da sauran ke karkashin fadar shugaban kasa da kuma ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Kashe-Kashen Jihar Filato: Sufeto Janar ya tsige Kwamishinan 'Yan sanda

Mafi akasarin wannan ma'aikatu na da muhimmancin gaske bangaren ci gaban kasa, kasuwanci, noma, kimiya da fasaha, cin hanci da rashawa da sauransu.

Kamar yadda shafin jaridar na Daily Trust ya bayyana, ko shakka babu akwai ma'aikatu da tuni shugaba Buhari ya nada jagororin su sai dai Majalisar Dokoki ta tarayya ba ta bayar da amicewar dangane da nade-naden ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel