Soyayyar uwa ya rikide: Wata Uwa ta hallaka Danta da wuta kan wayar Salula
Wata mata mai suna Chinenya ta hallaka Dan cikinta ta hanyar banka masa wuta saboda zarginsa da satar na’urar adanan bayanai na wayar salula, watau Memory card, kamar yadda gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Yuni a garin Abia na jihar Enugu, inda Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Ogbonna Geoffrey ya bayyana, inda yace sun samu nasarar kama Matar.
KU KARANTA: Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun: Kananan Yara 500 sun mutu a Zamfara
Dansadan yace Matar ta banka ma danta wuta mai shekaru 12, “Bayanai da muka samu sun nuna Matar ta aikata ma danta wannan danyen aiki sakamakon batar na’urar adanan bayanai na wayarta, daga nan ne ta kama yaron, inda ta daure shi, ta zuba kalanzir a hannunsa, ta cinna mar wuta.”
Sai dai Kaakakin yace duk da cewa an garzaya da yaron zuwa Asibiti, amma ba y nasara ba sakamakon tsananin kunar da ya samu, inda ya cika a ranar Talata, 26 ga watan Yuni, kamar yadda Kaakakin asibiti ya tabbatar.
Daga karshe Kaakakin Yansandan jihar yace zasu cigaba da gudanar da bincike, ya kara da cewa tuni suka mika gawar yaro zuwa dakin ajiyar gawarwaki na asibitin gwamnatin tarayya dake Umuhia.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng