Shugaba Buhari ya kaddamar da wani muhimmin aiki da ya sanya shi farin ciki
- Burin Shugaba ya fara cika a Najeriya
- Yau-yau ya kaddamar da wani gagarumin aikin da yayi murna da shi
- Har ma ya yabawa gwamnan jihar da gina aikin
Shugaba Muhammadu Buhari a yau Talata ya kaddamar da wani gagarumin aiki na kamfanin samar da irin shinkafa da gwamnan jihar Cross River ta gina a garin Calabar.
Muhammadu Buhari ya bayyana aikin a matsayin wata hanya ta marawa kudurin shirin kasar na farfado da aikin noma.
“A lokacin da mu ka hau mulki, mun kaddamar da mujalladin sarrafa kasar nan tahanyar samun kudade ba daga man fetir ba, saboda dora kasar a kan turbar rage dogaro da man fetur da kuma karfafawa sanya jari a sauran bangarori habaka tattalin arziki musamman noma”.
“Tabbas wannan kamfani ya nuna cewa muna samun nasara a yunkurinmu na mayar da alkiblar wannan kasar karkata zuwa bangaren noma”. Shugaba Buharin ya jaddada.
Sannan shugaban kasar yayi fatan kamfanin zai zamto wata sila ta habbaka noman shinkafa daga tan uku zuwa hudu a hekta guda ya dawo tan tara a hekta guda, kasancewar hakan zai taimaka matuka wajen sanya kasar nan ta iya samarwa da kanta shinkafar da ake bukata.
KU KARANTA: Buhari ya ba da umurnin sauya jami’an yan sanda a jihar Zamfara saboda tabbatar da tsaro
Daga nan ne shugaban ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa namijin kokarin da tayi na kafa kamfanin domin cigaban jihar, sannan ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ma’aikatar noma da su hada kai domin shigar da kamfanin cikin tsarin tallafin habaka noman shinkafa na kasa.
Ana shi jawabin gwamnan jihar ta Cross River Ben Ayade, cewa yayi duk wani yabo da za’a yi masa kan gina kamfanin to ya sadaukar da shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sannan ya kara da cewa gwamnatinsa ta samar da kamfanin ne domin magance matsalar karancin wadataccen nagartaccen takin shinkafa a jihar da ma kasa baki daya, kana ya shaidawa shugaban kasar cewa jihar a yanzu tana noman Audiga da Shinkafa da Masara da Ayaba da sauransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng