An nada sabon kwamishana a jihar Plateau

An nada sabon kwamishana a jihar Plateau

- Sufeto janar na hukumar yan sanda ya fatattaku kwamishanan yan sandan jihar

-Yan nada sabon kwamishana wanda aka tura daga Abuja

Sufeto janar na hukumar yan sadan Najeriya, IG Ibrahim Kpotun Idris, ya fatattaki kwamishanan yan sandan jihar, Undie Adie, bayan kisan akalla mutane 100 da ya faru karshen makon da ya gabata a jihar.

Sufeton ya nada CP Bala Ciroma ya maye gurbinsa da gaggawa.

An hallaka mutane akalla 100 a jihar sanadiyar rikici tsakanin yan garin Riyom da makiyaya inda yan Riyom suka tare hanya rana tsaka suna hallaka duk wanda suka gani da alaman Musulunci, cewan idon shaida.

An nada sabon kwamishana a jihar Plateau

An nada sabon kwamishana a jihar Plateau

A ranan Litinin, hukumar yan sanda da hukumar sojin sama sun tura jami’ai da jirage domin kawar da wannan kashe-kashe.

Daga baya aka sauya kwamishanan jihar. Domin tabbatar da hakan, kakakin hukumar yan sandan jihar, Terna Tyopev, yace Undie Adie ya rigaya da mika sandan mulki ga Bala Ciroma.

Yace: “A yau. 26 ga watan Yuni, 2018, sabon kwamishana CP Bala Ciroma ya zama kwamishanan yan sandan jihar Plateau,”

KU KARANTA: Hanyoyi 5 da zaku don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa

CP Bala Ciroma ya taba aiki a matsayin shugaban bangaren ayyuka na hukumar hana almudahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel