Yan sanda sun cafke wata mata bayan ta jefa jariri a masai

Yan sanda sun cafke wata mata bayan ta jefa jariri a masai

Rundunar yan sandan jihar Ogun sun ce sun kama wata matashiya mai shekaru 21, Amudalat Taiwo, kan laifin jefa jariri dan kwanaki 12 a masai a Ilaro, dake karamar hukumar Yewa South dake jihar.

Yan sandan sun ce an kama mai laifin ne bayan korafi da mai gidan da take haya, Oshunshina Olawale ya shigar.

Kakakin yan sandan, Abimbola Oyeyemi, yace mai gidan hayan ya kai karar cewa daya daga cikin masu haya a gidansa, gida mai lamba 28 unguwar Isheri, Ilaro ta tashi da safiyar ranar Lahadi, 20 ga watan Yuni, 2018 inda ta shiga bandaki amma bayan fitowarta sai aka ji kukan jariri daga cikin masan bandakin.

Yace bisa ga karfin korafin, jami’in dan sanda na yankin Ilaro, Opebiyi a ranar Lahadi, ya jagoranci jami’ai zuwa wajen, inda aka fasa masan sannan aka ceto jaririn.

Yan sanda sun cafke wata mata bayan ta jefa jariri a masai
Yan sanda sun cafke wata mata bayan ta jefa jariri a masai

Oyeyemi ya kara da cewa a lokacin bincike sun gano cewa mai laifin c eta haifi jaririn sannan suka kama shi.

Kakakin yan sandan yace mai laifin ta fadama yan sanda cewa ita marainiya ce, sannan kuma cewa ta auri wai Taiwo Owolabi, wanda yana da wata matar da yara biyar.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya bayar da tallafin N10m ga wadanda guguwar iska ya cika da su a Bauchi

Yace an kama mijin nata sakamakon kin daukewa iyalin nasa nauyin kuila da bai yi ba.

Daga karshe ya bayyana cewa yaron na nan cikin koshin lafiya a gidan marayu na Stella Obansanjo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng