Yanzu Yanzu: Osinbajo ya dira Plateau saboda kashe-kashen da ke faruwa

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya dira Plateau saboda kashe-kashen da ke faruwa

- A cigaba da nemo hanyar kawo karshen rikicin Plateau mataimakin shugaban kasa ya kai ziyara jihar

- Rikicin jihar dai yayi sandiyyar mutuwar mutane da dama wasu kuma sun jikkata

- Jami'an tsaro sun duka don ganin an dakile watsuwar rikicin zuwa sauran sassan jihar

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Plateau sakamakon rikice-rikicen da ya afku.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Yakubu Dati ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Jos ta hanyar wayar tarho.

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 86 da kuma wasu shida da suka jikkata a dalilin harin da aka kai tun 1:00pm na rana zuwa 8:00pm na dare a kauyukan jihar.

Yanzu- yanzu: Osinbajo ya dira Plateau saboda kashe-kashen da yake faruwa
Yanzu- yanzu: Osinbajo ya dira Plateau saboda kashe-kashen da yake faruwa

Da zarar mataimakin shugaban kasar ya sauka zai gana da masu ruwa da tsaki a jihar.

Sai dai wata majiya da ba’a tabbatar da sahihancinta ba ta fadi cewa an sake samun rahotan kai wani sabon hari kauyen Kwi kusa da filin jirgin sama dake karamar hukumar Riyom da yammacin yau Litinin. kamar yadda Premium Times ta rawaito.

KU KARANTA: Rikicin Plateau: Mutane sun fara kaura daga gidajensu

Majiyar ta ce maharan sun cinnawa kauyen da suka kai harin wuta wanda har wata tsohuwa ta rasu a sanadiyyar hakan.

Amma har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahotan, Legit.ng ta gaza samun sahihin bayanin da zai tabbatar da faruwar hakan ko akasinsa.

A yau din dai kuma kwamishinan ‘yan sanda na jihar zai gabatar da jawabi a gidajen talabijin da radiyo don shaida irin matakan da suke dauka don kawo karshen matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng